Sign in

RFI Hausa

@ha.rfi.fr
79 followers 6 following 8K posts

🌍 Sashen Hausa na RFI na maraba da ku a shafin Bluesky 💻 rfi.fr/ha/ 🎧 rfi.my/kai-tsaye 𝕏 rfi.my/Xha 📷 rfi.my/IGha 🗨️ rfi.my/WAha

PostsRepliesMedia
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 9h
EU ta ware Yuro miliyan 25 ga Libya don yaƙar kwararar baƙi zuwa Turai
rfi.my
EU ta ware Yuro miliyan 25 ga Libya don yaƙar kwararar baƙi zuwa Turai
Ƙungiyar tarayyar Turai ta faɗaɗa yarjejeniyar haɗin gwiwa da ta ƙulla da gwamnatin gabashin Libya don taimaka mata wajen daƙile kwararar baƙi zuwa nahiyar, inda ta aike wa ƙasar ta Afrika ƙarin kuɗi Yuro miliyan 25.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10h
Rungumar ci gaban zamani a Nijar ya haifar da koma baya ga kafafen sanarwa
rfi.my
Rungumar ci gaban zamani a Nijar ya haifar da koma baya ga kafafen sanarwa
Yanzu haka dai yawancin iyalai a Jamhuriyar  Nijar sun samar da dandali a shafukan sada zumunta don bada labari a tsakaninsu ko kuma tallata haja, wannan dai ya taimakawa iyalai da dama wajan rage kashe kuɗi wajan bayar da labarin haihuwa, suna, aure, rashin lafiya ko rasuwa da a baya ake amfani da kafafen radiyo ko talbijin ko kuma jaridu wajen sanarwa.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11h
Tsoffin sojojin Najeriya sun gudanar da zanga-zangar neman biyan haƙƙoƙinsu
rfi.my
Tsoffin sojojin Najeriya sun gudanar da zanga-zangar neman biyan haƙƙoƙinsu
Wasu fusatattun tsoffin sojojin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin ƙasar, Abuja, inda suka rufe hanyar shiga ofishin Hukumar Kula da Fansho riƙe da kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubucen koke-koke, tare da bayyana cewa tsadar rayuwa da matsin tattalin arziƙi sun jefa tsoffin dakarun cikin tsananin ƙunci saboda rashin biyansu alawus-alawus da sauran alfanun da doka ta tanada musu.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11h
An kama wasu manyan jami'ai da badaƙalar sace kuɗi biliyan 40 a Kamaru
rfi.my
An kama wasu manyan jami'ai da badaƙalar sace kuɗi biliyan 40 a Kamaru
A Kamaru an bankaɗo badaƙalar sace kuɗi na sama da biliyan 40 na man fetur da gwamnatin ke rabawa hukumar ƴan sanda jahohin ƙasar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11h
Sarkin Spain ya kai ziyara birnin Ceuta na ƙasar mai fama da rikicin tsaro
rfi.my
Sarkin Spain ya kai ziyara birnin Ceuta na ƙasar mai fama da rikicin tsaro
Sarki Felipe na shida na ƙasar Spain, tare da mai ɗakinsa Sarauniya Letizia, sun kai wata ziyara ta tarihi a birnin Ceuta na yankin Spain da ke kusa da Arewacin Afirka, karon farko da ya ziyarci yankin cikin kusan shekaru 20, kuma ziyarar na zuwa ne a matsayin nuna goyon baya ga mazauna birnin bayan wani babban rikicin jinkai da na tsaro da ya ɓalle a ƙarshen watan Yuli.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11h
Gwamnati Nijar ta sanar da fashewar wasu bututun mai da gas a Diffa
rfi.my
Gwamnati Nijar ta sanar da fashewar wasu bututun mai da gas a Diffa
A Jamhuriyar Nijar gwamnatin ƙasar ta sanar da fashewar wasu bututun ɗanyen mai da Iskar Gas a cikin dajin yankin Diffa, wanda jama’a suka jima suna yekuwar fashewarsa a hukumance.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12h
Tinubu ya sanya Wike da Soludo da Adeleke cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa
rfi.my
Tinubu ya sanya Wike da Soludo da Adeleke cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sake yin kwaskwarima ga kwamitin yaƙin neman zaɓensa, inda a wannan karon aka shigar da wasu gwamnoni da kuma sanatoci na jam’iyyun adawa, lamarin da ke zaman wani sabon abu a siyasar Najeriya.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 17h
Haifaffiyar Somalia Sagal Abdi-Wali ta zama ƴar Majalisa a Birtaniya
rfi.my
Haifaffiyar Somalia Sagal Abdi-Wali ta zama ƴar Majalisa a Birtaniya
Haifaffiyar Somalia Sagal Abdi-Wali ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabuwar ƴar Majalisar Birtaniya da ke wakiltar Holborn a St Pancras.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 17h
Tsohon shugaban Congo Kabila ya kafa sabuwar haɗaka da ƴan tawayen M23
rfi.my
Tsohon shugaban Congo Kabila ya kafa sabuwar haɗaka da ƴan tawayen M23
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Joseph Kabila ya ƙaddamar da wata sabuwar haɗakar siyasa da soji tare da ƙungiyar ƴan tawayen M23 mai samun goyon bayan Rwanda, wadda ta karɓe iko da akasarin sassan gabashin ƙasar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 18h
Lamurra sun daidaita a Tigray bayan sojojin Habasha sun karɓe iko da Mekelle
rfi.my
Lamurra sun daidaita a Tigray bayan sojojin Habasha sun karɓe iko da Mekelle
Lamurra sun fara daidaita a Mekelle babban birnin Tigray bayan da sojojin gwamnati suka kammala karɓe iko da yankin yayinda ƴan tawayen na TPLF suka fice zuwa garuruwan bayan gari a wani yanayi da tankiya ke tsananta tsakanin Habashar da maƙwabciyarta cike da fargabar yiwuwar ɓarkewar yaƙi.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 18h
Tattalin arziƙin Najeriya zai sake haɓaka yayinda Talakawa zasu ƙara talaucewa- IMF
rfi.my
Tattalin arziƙin Najeriya zai sake haɓaka yayinda Talakawa zasu ƙara talaucewa- IMF
Asusun bada lamuni na duniya IMF ya faɗaɗa hasashensa kan yiwuwar haɓakar tattalin arziƙin da Najeriya zata samu a shekarar nan zuwa kashi 4.2 kodayake ya kuma yi gargaɗi kan yadda hauhawar farashin kayakin masarufi ka iya sake jefa miliyoyin ƴan ƙasar a matsanancin talauci da ƙarancin abinci.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 19h
HRW ta buƙaci Senegal ta kawo ƙarshen tsauraran dokoki kan masu auren jinsi
rfi.my
HRW ta buƙaci Senegal ta kawo ƙarshen tsauraran dokoki kan masu auren jinsi
Ƙungiyar kare hakkin Ɗan Adam ta Human rights watch ta bukaci ƙasar Senegal da ta dakatar da aiwatar da dokokin haramta auren jinsi, ko mu’amala tsakanin mutane biyu masu jinsi ɗaya ko kuma yaɗa manufofinsu kafin lokacin gudanar da gasar wasannin guje-guje da tsalle-talle ta Olympics na matasa da za’a a gudanar a ƙasar cikin watan Nuwamba mai kamawa.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 19h
Ƴan tawayen Houthi sun ci gaba da kai hare-hare sassan Yemen da Saudiya
rfi.my
Ƴan tawayen Houthi sun ci gaba da kai hare-hare sassan Yemen da Saudiya
Ƴan tawayen Houthi na ci gaba da nausawa birnin Taiz na Yemen inda cikin sa’o’i 24 da suka gabata suka kai tarin hare-hare har a asibitin birnin wanda ya jikkata mutane a wani yanayi da ɗimbin jama’ar birnin suka bijirewa umarnin ƴan tawayen na barin gari cike da alwashin baiwa yankinsu kariya daga barazanar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Matatar Dangote ta tsawaita wa'adin sayar da hannayen jarinta a Afrika
rfi.my
Matatar Dangote ta tsawaita wa'adin sayar da hannayen jarinta a Afrika
Matatar Dangote ta tsawaita wa’adin da ta bai wa jama’a don sayen hannun jari a kamfanin da makonni biyu wato dai nan da 27 ga watan Oktoba, wanda a baya aka tsara rufe wa a gobe talata 13 ga watan Oktoba.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar lafiya da Amurka wadda ƙasashe da dama suka ƙaucewa
rfi.my
Najeriya ta ƙulla yarjejeniyar lafiya da Amurka wadda ƙasashe da dama suka ƙaucewa
Sabuwar yarjejeniyar lafiya ta dala biliyan 5 da Najeriya ta shiga tsakaninta da Amurka ta tayar da ƙura bayan da wasu ƙasashen Afrika suka ƙi shiga makamanciyarta sakamakon zargin tatsar bayanan ƴan ƙasarsu ba bisa ƙa’ida ba.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Najeriya ta cika shekaru goma ba tare da zartas da hukuncin kisa ba
rfi.my
Najeriya ta cika shekaru goma ba tare da zartas da hukuncin kisa ba
Najeriya ta cika shekaru goma ba tare da aiwatar da hukuncin kisa daga hannun gwamnati ba, lamarin da ya sake tayar da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na neman a samar da doka da za ta tabbatar dakatar da irin wannan hukunci a hukumance a ƙasar. 
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
INEC ta ƙaryata rahotannin yin gyara a jerin sunayen ƴan takarar gwamna da ta fitar
rfi.my
INEC ta ƙaryata rahotannin yin gyara a jerin sunayen ƴan takarar gwamna da ta fitar
A Najeriya ƴan ƙasar na ci gaba da shiga ruɗani bayan da hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakin sunayen jerin ƴan takara na ƙarshe ba tare da sunayen wasu ƴan takarar jam’iyyun adawa ba, ko da yake da fari hukumar ta musanta ingancin wannan takarda da ke yawo.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Mahukuntan Algeria sun cafke wasu ƴan Morocco 61 kan zargin zagon ƙasa
rfi.my
Mahukuntan Algeria sun cafke wasu ƴan Morocco 61 kan zargin zagon ƙasa
Mahukuntan Algeria sun tabbatar da cafke wasu 'yan Morocco 61 a farkon wannan wata, a bisa tuhumarsu da shirin aikata laifuka na yi wa ƙasa zagon ƙasa ta fuskar tsaro.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Gwamnatin Ghana ta ƙirƙiri sabuwar dokar haƙar ma'adinai a ƙasar
rfi.my
Gwamnatin Ghana ta ƙirƙiri sabuwar dokar haƙar ma'adinai a ƙasar
Gwamnatin ƙasar Ghana, ta amince da ƙirƙirar sabuwar dokar hakar ma'adinai, da nufin sauya fasalin yadda ake gudanar da harkokin hakar ma'adinai a ƙasar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Iran ta ce a shirye take ta shiga tsakani a rikicin ƴan Houthi da Saudiyya
rfi.my
Iran ta ce a shirye take ta shiga tsakani a rikicin ƴan Houthi da Saudiyya
Iran ta ce a shirye take ta shiga tsakani don sasanta rikicin mayaƙan Houthi na Yemen da kuma ƙasar Saudiyya, bayan munanan hare-haren da mayaƙan suka kai filin jirgin saman Riyadh da ya halaka mutane 14 a ƙarshen mako.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Tashin bam ya jikkata gwamman ɗalibai a Isra'ila
rfi.my
Tashin bam ya jikkata gwamman ɗalibai a Isra'ila
Aƙalla mutum guda ne ya mutu, wasu mutane 19 suka samu raunuka, bayan tashin wani bam a Isra’ila yau Litinin lokacin da wasu ɗalibai ke hawa tsaunuka a kusa da iyakar Lebanon.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata
rfi.my
Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi nazari kan matsalar birkicewar al’ada a tsakanin mata, matsala ce da ke matsayin ruwan dare a wannan zamani lura da cewa kusan dukkanin 1 cikin mata 3 akan iya samunta da wannan matsala wadda kuma ba safai aka fiya mayar da hankali akanta ba, duk kuwa da ƙalubalen hakan ga lafiyar mata.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Adadin fararen hular da ƴan tawayen Houthi suka kashe a Saudiya ya ƙaru zuwa 13
rfi.my
Adadin fararen hular da ƴan tawayen Houthi suka kashe a Saudiya ya ƙaru zuwa 13
Alƙaluman mutanen da suka mutu a harin ƙarshen mako da ƴan tawayen Houthi suka kai filin jirgin saman Riyadh na Saudiya ya ƙaru zuwa 13 ciki har da wani ɗan Falasɗinu da kuma ɗan Indiya a wani yanayi da ƙasashe irin Amurka da Asutralia ke gargaɗin al’ummominsu da su kaucewa balaguro ta filayen jirgin saman ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Gabas Ta Tsakiya.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Burkina Faso ta haramta fitar da abincin da manoma ke samarwa zuwa ƙetare
rfi.my
Burkina Faso ta haramta fitar da abincin da manoma ke samarwa zuwa ƙetare
Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da ɗaukar matakin haramta fitar da duk wani nau’in gari ko kuma fulawa da ake samarwa daga kayan hatsin da ake nomawa a  ƙasar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Nijar ta janye batun ƙara farashin man fetur da ya harzuƙa jama'ar ƙasar
rfi.my
Nijar ta janye batun ƙara farashin man fetur da ya harzuƙa jama'ar ƙasar
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai bayan da da farko ministan makamashi ya nuna yiyuwar hakan, inda ya ce gwamnati na kashe maƙudan kuɗi wajen sayo mai daga ƙetare don cike giɓin da ƙasar ke fuskanta.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekaru 83 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi
rfi.my
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekaru 83 da laifin safarar miyagun ƙwayoyi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya, ta sake kama wata tsohuwa mai shekaru 83 da aka bayyana sunanta da Uloma Sunday da laifin safarar ƙwayoyi, wanda ke matsayin karo na biyu cikin ƴan watanni da jami'an hukumar ke kame wannan tsohuwa wadda ta fito daga jihar Abia ta kudu maso gabashin ƙasar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 12/10/2026
Ana zargin Masar da kai harin da ya kashe masu haƙar ma'adinai 72 a iyakar Sudan
rfi.my
Ana zargin Masar da kai harin da ya kashe masu haƙar ma'adinai 72 a iyakar Sudan
Wasu masu haƙar Zinari aƙalla  72 ne suka gamu da ajalinsu, sakamakon hare-haren ta sama  da aka kai kan wani gun haƙar zinari da ke kan iyakar Sudan da Masar,lamarin da wata ƙungiyar Lauyoyin da ke fafutukan kare hakkin bil’adam a Sudan ta zargi Masar da kai harin da ya jikkata mutane da dama bayan waɗanda suka rasa ransu.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
An sake kai sabon hari filin jirgin saman Saudiyya sa'o'i bayan harin da ya kashe mutum 12
rfi.my
An sake kai sabon hari filin jirgin saman Saudiyya sa'o'i bayan harin da ya kashe mutum 12
Hukumomin tsaron ƙasar Saudiyya sun sanar da samun nasarar kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba kusa da filin jirgin saman King Khalid da ke birnin Riyadh, lamarin da ya janyo tsaiko na wucin gadi ga zirga-zirgar jiragen sama.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin baƙin haure sama da 130 a gaɓar tekun Djibouti
rfi.my
Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin baƙin haure sama da 130 a gaɓar tekun Djibouti
Aƙalla baƙin haure 139 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 84 suka ɓace bayan da wani kwale-kwale maƙare da mutane ya kife a gaɓar tekun Djibouti.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda 36
rfi.my
Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda 36
Hukumar Tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojin kasar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 36 tare da ceto mutane 50 da aka yi garkuwa da su a samamen da suka gudanar a sassan kasar daban-daban.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Wani ɗan bindiga kashe ƴan uwansa 7 ciki har da mai juna biyu a Amurka
rfi.my
Wani ɗan bindiga kashe ƴan uwansa 7 ciki har da mai juna biyu a Amurka
A Amurka, wani ɗan bindiga mai shekaru 45 ne ya kashe wasu ƴan uwansa 7 da aboki guda a wani gida a Pennsylvania, kafin daga bisani shima ya ɗauki rayuwarsa a ranar Asabar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Gwamnatin Nijar ta ce batada wani shirin ƙara farashin mai a ƙasar
rfi.my
Gwamnatin Nijar ta ce batada wani shirin ƙara farashin mai a ƙasar
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce batada wani shirin ƙara farashin litar mai a sassan ƙasar, a daidai lokacin da ake fuskantar dogayen layuka a gidajen man jihohi da dama, ciki har da birnin Yamai.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a jihohin Najeriya
rfi.my
INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a jihohin Najeriya
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta fitar da jerin sunayen mutanen da zasu yiwa jam’iyyu takarar gwamna a jihohi 28 na ƙasar da zasu shiga babban zaɓe na shekarar 2027.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Eritrea ta aike wa MDD wasiƙar neman shiga tsakani a rikicinta da Habasha
rfi.my
Eritrea ta aike wa MDD wasiƙar neman shiga tsakani a rikicinta da Habasha
Etitrea ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiga tsakani don sasanta rikicinta da maƙwabciyarta Habasha, inda ta ce zargin Addis Ababa na cewar dakarun Etitrea sun kutsa cikin ƙasar tamkar ayyana ɓarkewar yaƙi tsakaninsu ne.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Shugabannin duniya sun yi Allah wadai da harin mayaƙan Houthi a Saudiyya
rfi.my
Shugabannin duniya sun yi Allah wadai da harin mayaƙan Houthi a Saudiyya
Shugabannin ƙasashe da hukumomi a faɗin duniya sun fara mayar da martani a game da harin da mayaƙan Houthi suka ƙaddamar a Saudiyya jiya Asabar, inda suka bayyana goyon bayansu ga Riyadh.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 11/10/2026
Mayaƙan Houthi sun kai wa Saudiyya hari mafi muni da ta gani cikin shekaru 10
rfi.my
Mayaƙan Houthi sun kai wa Saudiyya hari mafi muni da ta gani cikin shekaru 10
Aƙalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu fiye da 300 suka jikkata bayan harin da mayaƙan Houthi suka kai filin jirgin saman Riyadh na ƙasar Saudiyya a ranar Asabar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Ukraine na buɓatar sabon shugaba domin Zelenskyy ya gaza - Trump
rfi.my
Ukraine na buɓatar sabon shugaba domin Zelenskyy ya gaza - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga al’ummar Ukraine da ta zaɓi sabon shugaba, inda ya zargi Volodymyr Zelenskyy da gazawa wajen tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da suke yi da Rasha, tare da bayar da gudunmawa wajen hauhawar farashin man dizal a Amurka.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Ƴansandan India ta kama sama da masu zanga-zanga dubu 15 a birnin New Delhi
rfi.my
Ƴansandan India ta kama sama da masu zanga-zanga dubu 15 a birnin New Delhi
Ƴansandan India sun kama tare da tsare ɗaruruwan mutanen da suka fito zanga-zaga ciki harda jagoransu a babban birnin ƙasar New Delhi, waɗanda ke neman shugaban hukumar zaɓen ƙasar yayi murabus daga matsayinsa.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Mutane kusan miliyan 4 aka tilastawa barin muhallansu a tsakiyar Sahel - UNHCR
rfi.my
Mutane kusan miliyan 4 aka tilastawa barin muhallansu a tsakiyar Sahel - UNHCR
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi game da yawaitar ƴan gudun hijira a tsakiyar yankin Sahel, inda ta ce an tilastawa kusan mutane miliyan huɗu barin gidajensu a ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Iyayen ɗaliban Oyo da aka sace a jihar Imo sun tabbatar da biyan kuɗin fansa
rfi.my
Iyayen ɗaliban Oyo da aka sace a jihar Imo sun tabbatar da biyan kuɗin fansa
Iyayen ɗalibai masu hidimar ƙasa 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Imo, sun tabbatar da cewar sai da suka biya naira miliyan shida-shida kafin a sako ƴaƴansu.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Sojojin Najeriya sun kunce wasu ababen fashewa 3 da aka dasa a jihar Zamfara
rfi.my
Sojojin Najeriya sun kunce wasu ababen fashewa 3 da aka dasa a jihar Zamfara
Dakarun da ke cikin rundunar Sojin Najeriya ta Operation Fansar Yamma mai yaƙi da ayyukan ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar sun sanar da nasarar lalata wasu ababen fashewa har guda 3 a jihar Zamfara.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Najeriya na laluben baƙar akwatin jirgin da ya yi haɗari tare da kashe Sojoji 32
rfi.my
Najeriya na laluben baƙar akwatin jirgin da ya yi haɗari tare da kashe Sojoji 32
A Najeriya, rundunar Sojin saman ƙasar ta ce ta fara laluben baƙar akwatin jirgin sojojinta ƙirar ATR-42 da ya yi haɗari a jihar Ondo lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa Lagos daga Benin cikin makon da muke bankwana da shi.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
Ana fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Habasha da Eritrea ƙasashe 2 maƙwabtan juna
rfi.my
Ana fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Habasha da Eritrea ƙasashe 2 maƙwabtan juna
Ƙasashen Habasha da Eritrea na zargin juna da faro yaƙi a tsakaninsu, bayan da a jiya Juma’a Habasha ta kai hari kan sojojin da Asmara ta girke a yankin Tigray, lamarin da ke nuna faro yaƙi tsakanin ƙasashen biyu da kai tsaye ke alamta yiwuwar rikicin wanda ya faro daga musayar zafafan kalamai ya iya juyewa zuwa rikicin yanki ba kaɗai yaƙi tsakanin ƙasashen biyu maƙwabtan juna ba.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 10/10/2026
IMF zai baiwa Nijar bashin dala miliyan 203 don tada komaɗar tattalin arziƙi
rfi.my
IMF zai baiwa Nijar bashin dala miliyan 203 don tada komaɗar tattalin arziƙi
Asusun bada lamuni na Duniya IMF ya tabbatar da cimma jituwa da mahukuntan Nijar don damƙawa ƙasar ta yankin Sahel bashin kuɗin da yawansu ya kai dala miliyan 203, cikin shekaru 3 masu zuwa, kuɗaɗen da ƙasar za ta yi amfani da su don samar da gyare a ɓangaren tattalin arziƙi.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Najeriya ta tsara dabarun gano ƙananan makamai a hannun mutane
rfi.my
Najeriya ta tsara dabarun gano ƙananan makamai a hannun mutane
Cibiyar horas da manyan hafsoshin soji a Najeriya da ƙungiyar shirya wasannin harbi a ƙasar sun ƙaddamar da wani gagarumin shirin ganowa tare da karɓe ɗimbin makaman jama’a suka mallaka ba a kan ƙa’ida ba a ƙasar. Muhammad Sani Abubakar na ɗauke da ƙarin bayani a wannan rahoto da ya aiko mana daga Abuja.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Kuɗin da jihohi ke samu daga gwamnatin Tinubu ya ƙaru da kaso 93 - Bankin Duniya
rfi.my
Kuɗin da jihohi ke samu daga gwamnatin Tinubu ya ƙaru da kaso 93 - Bankin Duniya
Bankin Duniya ya ce kuɗaɗen shiga da jihohin Najeriya ke samu ya ƙaru da kusan kashi 93 cikin ɗari tsakanin shekarar 2023 da 2025, bayan sauye-sauyen tattalin arziki, amma rahoton bankin ya nuna cewa kason da jihohin ke warewa fannin ilimi ya ragu zuwa kashi 12.1 a 2025 daga kashi 14.9 cikin ɗari a 2021.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Ƙasashen duniya sun bayyana goyan bayan su ga kotun ICC bayan barazanar Amurka
rfi.my
Ƙasashen duniya sun bayyana goyan bayan su ga kotun ICC bayan barazanar Amurka
Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar ƙasashen Turai da kuma wasu ƙasashe sun bayyana cikakkiyar goyan bayan su ga kotun duniya ta ICC, sakamakon takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata da kuma barazanar daƙile ayyukan ta.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Amurka za ta haske yadda za'a aiwatar da hukuncin kisa ga Hassan kai tsaye - Pentagon
rfi.my
Amurka za ta haske yadda za'a aiwatar da hukuncin kisa ga Hassan kai tsaye - Pentagon
Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce za ta nuna yadda za’a aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar bindige Nidal Hassan, mutumin da aka samu da laifin harbe mutane 13 har lahira a sansanin sojin Fort Hood a shekarar 2009.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Za mu wargaza haramtacciyar kotun duniya ta ICC – Rubio
rfi.my
Za mu wargaza haramtacciyar kotun duniya ta ICC – Rubio
Sa'oi kaɗan bayan sanar da tsohuwar mai shari'a a kotun duniya, Navi Pillay a matsayin wadda ta lashe kyuatar Nobel ta zaman lafiyar bana, gwamnatin Amurka ta bayyana sabbin takunkumi a kan alkalan kotun ta ICC.
000
RFI Hausa @ha.rfi.fr · 09/10/2026
Kaso 80 na namun dajin Afirka sun ƙare cikin shekaru hamsin - WWF
rfi.my
Kaso 80 na namun dajin Afirka sun ƙare cikin shekaru hamsin - WWF
Wani sabon rahoto da gidauniyar WWF dake sanya ido kan namun daji ta fitar, ya gano yadda adadin dabbobin dawa da ke nahiyar Afrika ya ragu da fiye da kashi 80 cikin 100 a tsakanin shekaru 50 da suka gabata.
000